Friday, December 5
Shadow

Wata Sabuwa: Sowore ya zargi ɗansanda da sace masa gilashi a wajen zanga-zangar ƴansanda

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Dan gwagwarmayar kare hakkin ɗan’adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya zargi wani ɗansanda da sace masa gilashin da mai ɗauke da na’ura a wajen zanga-zangar da aka yi a hedikwatar ƴansanda a Abuja a yau Litinin.

Zanga-zangar, wacce Sowore tare da wasu masu fafutukar kare hakkin bil’adama da tsoffin jami’an ‘yan sanda suka jagoranta, ta nemi a inganta walwalar jami’ai da kuma cire tsoffin jami’an daga tsarin fansho na haɗaka.

Daily Trust ta rawaito cewa a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta , Sowore ya bayyana cewa jami’in, wanda ke cikin kayan fararen hula, an kama shi a bidiyo yana aikata laifin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya musuluntar da wasu maguzawa

“Wannan jami’in rundunar ‘yansanda na Najeriya, cikin kayan fararen hula, ya sace min gilashin AI Rayban a hedikwatar rundunar yayin #ZangaZangarYanSanda yau. Manyansa suna kare shi. Don Allah a turo min saƙo idan kun san sunansa da mukaminsa cikin gaggawa!” in ji Sowore.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *