
Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta kama tare da lalata giya ta Naira Miliyan 5.8 a garin Kazaure.
Kwamandan Hisbah na jihar, Malam Ibrahim Dahiru ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN.
Yace shugaban karamar hukumar Kazaure, Alhaji Mansur Dabuwa ne ya jagiranci lalala giyar wadda ta kai kirate 400.
Yace shan giya a gaba dayan jihar haramunne kuma zasu ci gaba da yaki da hakan.