
Rahotanni sun bayyana cewa, wani muhimmin abu na shirin faruwa a siyasar Kano dama Najeriya baki daya.
Rahotannin na zuwane bayan da tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya kaiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ziyara a Abuja.
Ganawar tasu ta kasance ta sirri
Saidai bayan ganawar, Kwankwaso yace sun tattauna batun siyasa ne shi da Shugaban kasar, kuma yace akwai yiyuwar zasu yi aiki tare.
Saidai bai kara cewa komai game da hakan ba.
Dama dai tuni rade-radi suka yi yawa cewa Kwankwaso na shirin komawa APC.