Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Fitar Da Bayani Kai Tsaye Kan Zargin Sauya Shettima, Inji Baba Ahmad

Daga Muhammad Kwairi Waziri
Baba-Ahmed ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kamata shi da kansa ya fito ya musanta zargin da ake yi na shirin sauya mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima. Ya ce hakan zai taimaka wajen kwantar da hankulan jama’a da kawo karshen jita-jita marasa tushe.
Ya kara da cewa, idan Shugaba Tinubu ya yi wannan bayani kai tsaye, zai nuna gaskiya da jajircewa wajen tafiyar da mulki cikin kwanciyar hankali da tsari.