
Rahotanni sun bayyana cewa, a jiya Laraba an samu wata dambarwa tsakanin kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da sanata Opeyemi Bamidele.
Muhawarar tasu ta yi zafi sosai ta yanda kiris ya rage su gwabza.
Hakan ya farune a yayin da ake zaman taron shuwagabannin majalisar wanda suke tattauna ko su tafi hutu da suka saba tafiya ko kuwa a’a.
A yayin zaman, Sanata Ali Ndume ya soki shugabancin Sanata Godswill Akpabio wanda hakan yasa shima sanata, Opeyemi Bamidele ya tashi yace shima bai jin dadin shugabancin Akpabio.
Akpabio ya tashi tsaye yana cewa, shine shugaban majalisa kuma babu wanda ya isa yayi magana idan yana magana.
Ya kuma kare kanshi bisa zargin da ake masa inda yace yasan aiki sosai yayi kwamishina yayi gwamna sau biyu, yayi babban minista yayi shugabanci a majalisar dan haka babu wanda zai gaya mai sanin aiki.