Friday, December 5
Shadow

Tinubu yayi watsi da Arewa, kudu yake ta rayawa>>Inji Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya caccaki gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.

Kwankwaso yace Tinubu ya mayar da hankali wajan kai abubuwan ci gaba kudu yayi watsi da Arewa.

Kwankwaso ya bayyana bakane a yayin taron masu ruwa sa tsaki na jihar Kano inda ake tattauna batun gyaran kundin tsarin mulki.

Yace da ya je Abuja ta jirgi ya so ya dawo amma sai aka samu matsala ya dawo ta Mota, yace titin Abuja zuwa Kaduna bashi da kyau ko kadan

Kwankwaso yace amma Gwamnatin Tinubu na gina titi daga jihohin Yarbawa zuwa jihohin Inyamurai.

Yace basa sukar yiwa jama’a aiki a kowane sashe na Najeriya amma a mayar da hankali wajan yiwa wani bangare aiki yayin da aka yi watsi da wani bangare hakan bai kamata ba.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Tinubu yayi hannu da hannu da sabon Fafaroma na duniya a birnin Rome na kasar Italiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *