
Rahotanni sun tabbatar da cewa, Hukumar tsaro ta DSS ce suka kama matashi Sultan me watsa labarai a Tiktok daga gidansa inda suka wuce dashi Abuja.
Asalin sunan Sultan shine Ghali Isma’il kuma a ranar Juma’a watau Jiya aka gurfanar dashi a gaban kotun Magistre dake Abuja bisa zargin yayi ikirarin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mutu.
Sannan an zargeshi da cusawa ‘yan Najeriya kiyayyar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Dan haka alkalin kotun yasa aka tafi dashi zuwa gidan gyara hali na Keffi.
Ismail dan shekaru 29 wanda dan asalin garin Jogana ne na karamar hukumar Gezawa jihar Kano.
An zargeshi da cewa, yayi ikirarin samun bayanai cewa wai ahugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ci guba a abinci ya mutu.
An zargeshi da dora Bidiyon a shafin Tiktok me sunan @bola_asiwaju
Kotun dai ta hana belin Sultan inda ta daga ci gaba da sauraren karar sai nan da ranar August 19, 2025.
Saidai a martani kan hakan.
Shima shahararren dan Tiktok, Aminu J Town ya bayyana cewa Bidiyon da sultan yayi ba akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bane.
Akan shugaban kasar Israyla ne watau Benjamin Netanyahu.