
Malamin Addinin Islama, Baffa Hotoro ya caccaki babban malamin Addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami bayan da Pantamin yace rike Charbi ba bidi’a bane.
Pantami yace Amfani da charbi ba laifi.
Sannan ya kara da cewa duk malamin da yake da ja, yana maraba dashi.
Anan ne shi kuma Baffa Hotoro yace ya karbi wannan kalubale na malam Pantami inda yace idan Pantami yaki to lallai sauran mutuncin da ya rage masa zai zube.