
Kungiyar ‘yan matan Najeriya dake buga kwallon kafa, Super Falcons sun lashe kofin gasar mata na nahiyar Africa bayan doke kasar Morocco da ci 3-2.
Wani bin mamaki shine, Har aka ke hutun Rabin lokaci, Morocco na cin Najeriya 2-0 wanda ana tunanin wasa ya kare.
Saidai bayan a aka dawo hutun rabin lokacine ‘yan Matan Najeriya suka nina azama suka rama kwallayen har suka kara kwallo daya a ragar Morocco wanda a haka aka tashi wasan 3-2.
Bayan nasarar tasu, Shugaba Tinubu ya kirasu a waya inda ya bayyana farin cikinsa da shaida mus cewa, Najeriya na Alfahari dasu.