
Jihohin da Gwamnonin APC ke mulki guda 11 sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin samar masa kuri’u Miliyan 15.2 a zaben shekarar 2027.
Jihohin Arewa ta tsakiya, Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, Plateau ne suka farawa yiwa shugaban Alkawarin kuri’u Miliyan 6.
Sun bayyana hakane ta bakin wakilinsu, Saleh Zazzaga, hakan na zuwane bayan da aka baiwa Prof. Nentawe Yilwatda mukamin shugaban jam’iyyar APC.
Hakanan jihar Akwa-Ibom ta yiwa shugaba Tinubu Alkawarin kuri’u Miliyan 3.5.
Daga jihar Edo Kuwa Gwamna Monday Okpebholo yawa Tinubu alkawarin kuri’u Miliyan 2.5.
Jihar Benue tawa shugaban Alkawarin kuri’u Miliyan 2.
Daga jihohin Oyo da Ekiti kuwa kuri’u Miliyan 1.2 sukawa shugaba Tinubu Alkawari.