
Mawaki, Aminu J. Town ya bayyana cewa, Haka harkar fim take ba’a gama ta lafiya.
Ya bayyana hakane a wani podcast da aka yi dashi inda yace ko dai mutum yayi mutuwar wulakanci ko kuma a zo ana nema mai taimako haka ‘yan fim ke karewa.
Hakan na zuwane bayan dambarwar tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu wadda ta bayyana a shirin Gabon Show abin tausai
Tuni dai har an fara taimakawa Ummi Nuhu ganin halin data tsinci kanta.