
An yi caaa akan tsohuwar Tauraruwar fina-finan Rukayya Dawayya bayan da ta daki Bidiyo tana habaici anda da yawa suka fassara da cewa, da Ummi Nuhu take.
Dawayya ta saki Bidiyo tana fadin cewa, Wasu a lokacin da suke ganiyarsu aun raina mutane har ma iyayensu basa jin maganarsu, sannan kuma ko Ibada basa yi.
Saidai duk da Dawayya bata kira suna ba, da yawa sun fassara cewa da Ummi Nuhu take.
Wata me suna Zinariya a Tiktok har kafe hoton Dawayya tayi tana cewa, ko dai itace abokiyar fadan Ummi Nuhu?
Tace dai ko ma me Ummi Nuhu ta yi a yanzu ta yi nadama kuma ya kamata ya wuce.
Dama dai a hirar da Gabon ta yi da Ummi Nuhu ta bayyana cewa, wasu na ta kallonta da abinda ta aikata a baya.