
A baya dai Mun ga Bidiyon yanda Sheikh Nura Khalid, Digital Imam ya fito yawa ‘yan Izalar Jos raddi kan abinda ya kira kazafin da suka masa da Sheikh Bawa Mai Shinkafa.
Daga baya babban dansa ya fito shima yayi raddi inda yace ba zasu yafe abinda akawa Mahaifinsu ba.
Hakanan a yanzu Karamin dansa ya sake fitowa yace wanan magana sai sun kai ta kotu.
Ya fito cikin kuka yana fadar cewa abinda ake musu ya isa haka.
Lamarin ya baiwa mutane mamaki matuka.