Friday, December 5
Shadow

Ba zan koma APC ba amma akwai yiyuwar in yiwa Tinubu aiki>> Inji Kwankwaso

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ba zai koma jam’iyyar APC ba.

Kwankwaso ya bayyana hakane ta bakin jam’iyyar sa ta NNPP inda ta karyata cewa yana shirin barin jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC.

Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da aka ga Kwankwaso a fadar shugaban kasa wanda an yi tsammanin ganawa yayi da shugaban kasar amma majiya me kyau tace basu gana ba, kamar yanda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Prince Nweze Onu ya bayyana cewa labarin komawar Kwankwaso APC kirkirarsa aka yi aka dora a kafafen sada zumunta ta hanyar Amfani da AI.

Karanta Wannan  Yanda me dafa babbar tukunyar Shinkafa ta Najeriya, Hilda Baci ta taka cikin tukunyar ta kuma wanke ta da Mofa ya jawo cece kuce

Ya kuma bayyana cewa, ziyarar Kwankwaso a fadar shugaban kasa da aka gani ba zama ya je yi da Tinubu ba, taro ne ya kaishi, kamar yanda kafar PMnewsNigeria ta ruwaito.

Saidai a ranar 21 ga watan Yuli, Jaridar Punchng ta ruwaito Kwankwaso na cewa akwai yiyuwar su yi aiki tare sa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *