Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyo: Mutum kamar Buhari saboda Jahilci ku saka masa Fulawa a kabarinsa, Ko dai dama murna kuke da rashinsa?>> Albanin Gombe ya caccaki Iyalan Buhari

Babban Malamin Addinin Islama, Albanin Gombe ya bayyana rashin jin dadi game da fulawar da iyalan Tsohon Shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari suka sanya a kabarinsa.

An dai ga yanda akai ta gyara kabarin tsohon shugaban kasa daga na kasa aka zagayeshi aka daga gini aka kuma saka Interlock aka zagayeshi.

Bayannan kuma an ga yanda aka saka Fulawa aka zagaye kabarin.

Malam Albanin Gombe yace Fulawa dai alamar Murna ce dan haka ko dai iyalan tsohon shugaban kasar Murna suke da Rashinsa?

Ya yi kira ga A’isha Buhari data tuntubi malaman data yadda dasu game da saka fulawar.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tinubu ta dakatar da gina sabbin makarantun Jami'a na tsawon shekaru 7 inda tace akwai makarantun jami'a da malamai sun fi dalibai yawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *