Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, yasan matakan da gwanatinsa ta dauka na tayar da komadar tattalin arziki sun kawo wahala.
Ya bayyana hakane a jawabin da yayi da safiyar yau na ranar Dimokradiyya.
Inda yace yana sane da wahalar da ‘yan kasa suke sha.
Ya bayyana cewa amma daukar matakan dolene dan dora Najeriya a turba me kyau wadda zata daina dogaro akan man fetur kadai dan samun kudin shiga.
Ya bayyana cewa wannan abu ne da ya kamata a yi shi da dadewa amma shuwagabannin da suka gabata ba su yi ba.