Friday, December 5
Shadow

Shugaba Tinubu na nuna tausai sosai a mulkinsa>>Inji Kashim Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na nuna tausai sosai a mulkinsa.

Ya bayyana hakane a wajan taron da aka gudanar a Arewa House dake Jihar Kaduna.

Kashim Shettima wanda me baiwa shugaban kasa shawara kan ayyuka na musamman, Dr Aliyu Modibbo Umar, ya wakilta a wajan taron da aka yi na kwanki biyu, ya bayyana cewa shugaban kasar ya kawo ayyukan ci gaba sosai.

Ya bayar da misali a bangaren Ilimi inda yace shugaba Tinubu ya samarwa ‘ya’yan talakawa damar karatu inda aka rika bayar sa bashin karatu.

Yace daga baya da aka ga cewa, Guarantor da kuma kayyade yawan samun mutum kamin a bashi bashin zai zo da matsala sai aka dakatar da hakan aka rika baiwa daliban bashin kai tsaye.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon:Sheikh Lawan Triumph yayi Allah ya isa ga abinda tawagar Sarki Sanusi II suka yi a kofar gidan Aminu Dogo Dantata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *