
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ya bayyana rashin jin dadinsa kan yanda ga ci gaba Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na kawowa amma ‘yan Najeriya da yawa basa gani.
Ministan ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Yace Najeriya a yanzu tafi baya ci gaba sannan a yanzu an samu tsaro fiye da da.
Ya kara da cewa tattalin arziki na bunkasa wanda har kasashen Duniya sun shaida hakan.
Wannan jawabi nasa na zuwane a yayin da ‘yan Najeriya da yawa ke kukan matsin rayuwa.