
Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa ‘yan Najeriya basu taba shan irin wahalar da suke sha a gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na Channels TV.
Yace wasu har bola suke bi suna tsintar Abinci.
Melaye yace mutum idan yana son ya gane irin wahalar da ake ciki, ya je kauye, mutane na ta mutuwa saboda tsananin rashin abinci.
Da yake magana akan jam’iyyar PDP, Sanata Dino Melaye yace APC ta rika ta saye jam’iyyar PDP da hakan PDP ba jam’iyyar dogaro bace.