
Matatar man Dangote ta nada David Bird mukamin CEO wanda zai jagoranci gudanarwar matatar.
S&P Global ne suka ruwaito hakan inda suka ce David Bird zai fara aiki a Watan Yuli.
Rahotanni sun ce David Bird Kwararren Injiniya ne wanda yayi aiki da kamfanin Shell na tsawon kusan shekaru 20.
Saidai har yanzu Dangote zai ci gaba da zama a matsayin mamallakin matatar man.