
Rahotanni sun tabbatar da cewa kungiyar malaman jinya(Nurse) da Ungozoma ta Najeriya,(NANNM) sun janye yajin aikin gargadin da suke.
Sanarwar janye yajin aikin na kunshene a cikin takardar da shugaban kungiyar, Haruna Mamman da babban sakatarenta, T.A Shettima suka sakawa hannu.
Tun ranar Laraba ne dai kungiyar ta fara yajin aikin bayan karewar kwanaki 15 da ta baiwa gwamnati ta biya mata bukatunta.
Yajin aikin ya zo karshene bayan ganawar da kungiyar ta yi a yau Asabar.
A ranar Juma’ar data gabata, kungiyar ta yi zama na musamman da wakilan Gwamnati.