
Wani Dan Kannywood ya fito ya bayyana cewa, Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa Ummi Nuhu ba abin tausai bace dan kuwa babu abinda ba’a mata na taimako ba a baya.
Yace asalin matsalarta ta fara ne da tsinuwar da mahaifiyarta ta mata.
Yace Farida Jalal Shaidace duk da tana dakin mijinta ba lallai ta fito ta yi magana ba amma itace ta je gidan su Ummi Nuhu ta ga suna sa insa da mahaifiyarta akan ta debo abinci, anan mahaifiyar ta yi mata baki.
Yace daga nan ne suka kama hanyar tafiya inda a wannan tafiyar ne suka yi hadari ta kakkarye.
Yace Ali Nuhu har albashin Naira dubu 100 ya mata sannan akwai sauran wadanda suka taimaketa amma saboda hanyar rayuwar data dauka ba me dorewa bace shiyasa duk kowa ya gaji aka kyaleta.
Yace Ummi Nuhu ba abin tausai bace wadanda ya kamata a tausayawa sune irin su moda.