
Tauraruwar Kannywood, Samha M. Inuwa ta bayyana cewa, Hadarin motar da ya rutsa da ita jiya a hanyarta ta komawa Gida Kano daga Kaduna inda ta halarci wajan bikin Jamilu Adamu Kochila tace jiface.
An ga yanda motar su Samha ta daki Tirela ta baya inda ta lalace, Samha tace idan aka ce mata mutum ya fita da rai daga cikin motarnan zaka yi mamaki amma Saboda addu’ar iyaye, Allah ya tsallakar da ita daga hadarin.
Saidai tace duk da wannan abin da ya faru da ita, ba zata daina kyauta ba.