
A wajan Bikin Dan Kannywood, Jamilu Adamu Kochila wanda aka yi a Kaduna, Samha M. Inuwa ta bayar da kyautar Dalar Amurka 100.
An ga yanda Samha ke rawa inda ta ciro dala 100 a jakarta ta mikawa wani kyauta.
A hanyarta ta dawowa gida Kano, daga Kaduna, An ga yanda Samha ta yi mummunan hadarin mota wanda motar tasu ta daki bayan Tirela.
A Bidiyon Samha da aka gani bayan Hadarin, Tace Jifa ce aka mata daga kawai ta yi kyautar Dala $100. Samha tace Addu’ar Iyaye ce ta tseratar da ita.
Saidai Samha tace ba zata daina kyauta ba duk da abinda aka mata.
Karanta Wannan SHEIK DAHIRU BAUCHI: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A Duniya