
Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa shine na daya wajan cika Alkawarin gudummawar kudi a wajan bikin tauraron Kannywood, Jamilu Kochila.
Ahmed Musa, yayi alkawrin bayar da Naira Miliyan 5.

Kuma a jiya, Mansurah Isah ta wallafa Rasit din shaidar cika alkawarin da yayi.
Mansurah ta kara da cewa zasu fara wallafa sunan wadanda suka cika Alkawarin da suka dauka.

Saidai itama Sadiya Kabala ta bayyana cewa, Daga yanzu idan aka je wajan Biki zata tashi tace ta bada gummawar Naira kaza sai ta yi fuska kawai.

Hakan dai alamu ce dake nuna cewa, da yawa basu cika alkawuran da suka dauka a wajan bikin ba.