Nafisa ta cancanci kyautar Dala 100,000 da gida da lambar OON – Farfesa Pantami

Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa Nafisa Abdullahi wadda ta lashe gasar Turanci ta duniya ta cancanci kyautar Dala 100,000 da kuma gida da lambar yabon OON.
Pantami ya bayyana haka a wani rubutu da ya wallafa a yau Talata a shafinsa na Manhajar Facebook.