
Dan majalisar tarayya daga Zamfara Kabiru Mai Palace ya gayara makabartu 80 a jihar.
Da yake magana da manema labarai ranar Talata wajan kaddamar da aikin, yace kowane mutum idan ya rasu makabarta za’a kai a binneshi.
Makabartun da aka gyara na tsakanin kananan Hukumomin Tsafe da Gusau ne
Ya kuma bayyana cewa gyaran ya zama dole lura da halin lalacewa da makabartun suke.
Ya sha Alwashin daukar masu gadin makabartar da kuma biyansu Haraji.