
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Abdallah Gadon kaya yayi kiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya karrama yara mata da suka yi nasarar lashe gasar Turanci ta Duniya tare da iyayensu.
Yace ya kamata a karrama hadda iyayensu saboda yanda suka kula dasu suka basu tarbiyya da ilimi da har suka kai wannan mataki.
Malam yace ba ‘yan kwallo kadai shugaban kasar zai rika karramawa ba.
inda yace shugaban zai bar mummunan tarihi idan bai karrama wadannan yara ba.
Wannan kira na malam na zuwane bayan na Sheikh Isa Ali Pantami na cewa ya kamata shugaba Tinubu yawa yaran irin karramawar da yawa ‘yan Kwallon Najeriya.