
Jam’iyyar APC Reshen jihar Kano ta baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tabbacin goyon baya a zaben shekarar 2027 me zuwa.
Jam’iyyar ta kuma bayyana Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar.
Sun bayyana hakane yayin wani zama da aka yi a gidan tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Abdullahi Abbas ya bayyana cewa, an shirya taronne dan warware matsalolin cikin gida na jam’iyyar da kuma shiryawa babban zaben shekarar 2027 dake tafe.