Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Farfaɗo da Masaku a Kaduna don Inganta Tattalin Arziki Da Ayyukan Yi

Gwamnatin Tarayya Ta Fara Shirin Farfaɗo da Masaku a Kaduna don Inganta Tattalin Arziki Da Ayyukan Yi.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kaddamar da wani shiri na farfaɗo da masana’antun auduga, masaku da tufafi a ƙasar, inda ƙaramin Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Sanata John Enoh, ya kai ziyara jihar Kaduna domin duba muhimman masana’antun da suka shafi bangaren.

Ministan ya bayyana cewa sake farfaɗo da waɗannan masana’antu zai taimaka matuka wajen habaka tattalin arzikin ƙasa da samar da ayyukan yi ga matasa da ma sauran ’yan ƙasa.

Bayan gudanar da wannan ziyara ta gani da ido, Sanata Enoh ya halarci wani taro tare da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi wajen dawo da martabar masana’antun sarrafa auduga da samar da tufafi a Najeriya. Ya jaddada muhimmancin sake farfaɗo da kamfanin United Nigerian Textiles Limited (UNTL) da ke Kaduna, yana mai cewa hakan zai kara wa masana’antun masaku kwarin gwiwa da kuma farfado da harkokin masana’antun gaba ɗaya.

Karanta Wannan  An saci Naira Miliyan 329 daga bankunan Najeriya ta hanyar amfani da BVN na Jabu

A nasa jawabin a yayin taron, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana damuwarsa kan yadda masana’antar UNTL ta tsaya cak tun shekarar 2022. Ya danganta haka da tabarbarewar tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar, yana mai bayyana cewa masana’antar na da tarihin samar da fiye da guraben ayyukan yi dubu goma (10,000) a fannoni daban-daban, kafin durkushewarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *