
Rahotanni sun bayyana cewa, iyaye na neman a soke jarabawar WAEC ta bana saboda yanda aka fadi jarabawar da yawa.
Ba iyayen kadai ba hadda kungiyar dalibai ta kasa, NANs ta bayyana rashin jin dadi kan sakamakon jarabawar na bana.
Sun bayyana musamman damuwa ga jarabawar Turanci wadda aka rubutata a lokuta marasa dadi.
Jarabawar ta bana dai an ga yanda aka rika rubuta wasu jarabawowin a cikin duhu.
Shin ko WAEC zata yadda da wannan kira?
Saidai a jira a gani.