
Fasto Ayodele ya bayyana cewa, Peter Obi idan ba hakuri yayi ya zama mataimakin shugaban kasa ba, ba zai taba zama shugaban kasa ba.
Hakanan yace shima Nuhu Ribadu sai ya koma Adamawa ya zama Gwamna kamin ya samu nasarar zama shugaban kasa, Saidai yace mutanen Adamawa basa son Nuhu Ribadu dan haka ba zai iya nasarar zama Gwamna ba.
Peter Obi dai shine yayi takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 a jam’iyyar Labour party inda ya zo na 3.
Hakanan Nuhu Ribadu ana rade-radin shine zai yi takara a APC idan Tinubu ya kammala wa’adinsa na shekaru 8.