“Wallahi Aure Nake So Amma Babu Hali Saboda Maraicina”

“Sunana Rabi’atu Rabi’u. Ni ‘ýar garin Gwarzo ce, Unguwar mu daya da mataimakin Gwamnan Kano.
Jama’a Wallahi Aure nake so, na jima da isa aure, saidai na kasance marainiya, mahaifina ya rasu mahaifiyata karfin ta ya kare abibda za mu ci ma wahala yake yi mana.
Shi yasa nake rokon al’umma don Allah su taimaka su yi min aure ko su yi min kayan daki sabida bana so halin da nake a ciki ya jefa ni cikin hàŕķar bànźa.
Saboda akwai tashin hankali a ce mace kamar ni ina son aure amma babu halin a yi min aure.
Daga Nasiru S. Abdullahi