Friday, December 5
Shadow

Dan Sarkin Kano, Adam Muhammad Sanusi ya ce mutane su daina zargin babansa kan wahalar da suke ciki da maganar cire tallafin man fetur inda wasu ke ganin kamar baban nasa ne ya zuga aka cire tallafin

Dan gidan sarkin Kano, Adam Lamido Sanusi ya jawo hankalin masu sukar mahaifinsa game da cewa shine ya zuga aka cire tallafin man fetur dan haka ake zarginsa da wahalar da ake ciki.

Yace ba gaskiya bane, babansa bai bayar da shawarar cewa a cire tallafin man fetur a lokaci guda ba.

Yace da an cire tallafin man fetur din tun a lokacin da mahaifiyarsu ya bayar da shawarar a cire tallafin da ba’a shiga wahalar da ake ciki ba.

Ya kara da cewa, Biyan Tallafin man fetur ya lakume kudin Najeriya gaba daya ta yanda sai an rika ciwo bashi ake iya biyan tallafin.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Naira Miliyan 2 Soja Boy yake baiwa 'yan mata suna rawa dashi a wakokinsa na Badhala

Yace kuma mutane na karya su ce sun shigo da man fetur daga kasashen waje dan a basu tallafin.

Yace kuma ana daukar man fetur dun na Najeriya da aka biya tallafi akansa akai shi kasashe makwabta a rika sayarwa da tsada.

Ya bayyana hakane a shafinsa na X.

Inda yace cire tallafin da hadashi da tsare-tsaren matsin tattalin arziki ne ya haifar da wahalar da ake ciki wanda mahaifinsu bai bayar da shawarar a yi hakan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *