
A kwanakin bayane dai Bidiyon rawar gwamnan jihar Naija, Umar Bago ta jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta inda aka ganshi yana rawa da wakar da Rarara yawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu me suna Omologo.
A wancan karin wasu sun yaba inda wasu kuma da yawa suka kushe da cewa a matsayinsa na shugaba, hakan bai dace ba.
A wannan karin ma kuma sai gashi aka sake ganin Gwamna Bago yana rawa.
Shima dai a wannan karin mutane basu yi shiru ba, an ci gaba da kushe.