Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyo: Sabbin Motocin dakon man fetur da Dangote ya siyo sun iso Najeriya har a kai masa kamfaninsa

Rahotanni sun bayyana cewa, Sabbin Motocin dakon man fetur na Dangote sun iso Najeriya inda tuni aka fara kai masa su kamfanin nasa.

Wannan na daga cikin shirin matatar man fetur ta Dangote na fara yin dakon Man fetur din zuwa gidajen man fetur da motocin maimakon amfani dana ‘yan kasuwa.

Jaridar Vanguard tace motocin sun bar Tashar jiragen ruwa ta Apapa inda aka kaisu matatar man fetur din dake Ibeju-Lekki.

Rahoton ya kara da cewa ma’aikatan matatar man fetur din sun rika shewa da murna bayan ganin zuwan motocin.

Hakan na zuwane yayin da kungiyar direbobin Tanka ta Najeriya ke adawa da wannan shiri inda suka ce Dangoten ba zai iya wadata kowane bangare na Najeriya da motocin nasa ba.

Karanta Wannan  Hukumar EFCC Ta Kama Wani Ma'aikacin Gwamnati Saboda Ya Yaga Takardar Tuhumarsa Da Aka Kai Masa

Sun yi zargin cewa, Dangote na son ya zama shi kadai ne ke da ruwa da tsaki a harkar man fetur a kasarnan inda suka nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka baki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *