Friday, December 26
Shadow

Amarya, Rahama Sadau ta godewa ‘yan Uwa da abokan arziki da suka tayata Biki

Tauraruwar Fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta mika sakon godiya ga ‘yan uwa da abokan arziki da suka tayata Biki.

Rahama ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta inda tace bata da kalaman godiya da zata iya bayyana irin farin cikin da take ciki.

“Ina mika sakon godiya ta musamman ga dangi, ’yan uwa da abokan arziki bisa fatan alheri da addu’o’in ku a game da Auren mu. Kalmominku da addu’arku sun karfafa mana guiwa kuma sun sa ranar ta kasance ta musamman. Allah Ya saka da alkhairi.

Bani da kalmomin yi muku godia sai dai nace Allah ya saka muku da alheri, Allah yabar zumunchi na gode, na gode, Allah ya biyawa kowa bukatun sa na alheri. Ameen

Karanta Wannan  JAMB ta saka sabuwar ranar fara jarrabawar wannan shekara

Ni kuma Allah ya bamu zaman lafia da Miji na Allah ya Albarkachi rayuwar auren mu. Ameen ya rabbil Alameen.

Ina yiwa kowa fatan alheri.

Bissalam.

HappilyMarried #Mrs #RahamaSadauNowAMrs #LoveTriumphs #OffTheMarket #BlessedBeginnings

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *