
Masu laifi 16 ne suka tsere daga gidan gyara hali na Keffi dake jihar Nasarawa
Lamarin ya farune da sassafiyar ranar Talata.
Me magana da yawun hukumar kula da gidajen gyara hali na kasa, Umar Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace jami’an hukumar 5 ne suka jikkata sanadiyyar lamarin.
Yace 2 daga ciki suna cikin mawuyacin hali
Saidai yace an kama 7 daga cikin wadanda suka tsere kuma ana bin sahun sauran.