Friday, December 5
Shadow

Kotu ta cewa Gwamnatin tarayya ta kawo karshen Shari’ar Dasuki

Kotu ta ba gwamnatin tarayya wa’adin Satumba kan shari’ar Dasuki.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin zuwa ranakun 24, 25 da 26 ga watan Satumba domin kammala shari’ar tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro , Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya), kan zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da badakalar kudi.

Mai shari’a Peter Lifu ya umurci gwamnati ta kammala kiran shaidu da gabatar da dukkan shaidun da za ta dogara da su a shari’ar da ta fara tun 2015.

A zaman baya, kotu ta karbi kayayyakin da aka samo daga gidajen Dasuki a Abuja da Sokoto a matsayin shaida, ciki har da kwamfuta, wayoyi, kudi da takardun banki.

Karanta Wannan  Bazan goyi bayan Gwamnatin Tinubu ba>>Sarki Sanusi II

An dage shari’ar zuwa Satumba domin gwamnati ta rufe gabatar da shaidu sannan Dasuki ya fara kare kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *