
Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana cewa, mutane na mamakin tace an bata kwangilar Naira Biliyan 4.
Tace abinda da yawa basu fahimta ba shine, ba wai Biliyan 4 tsabar kudi ake magana ba, ana maganar a rubucene.
Tace idan tsabar kudi ake magana, ko Dangote da me kudin Duniya, Elon Musk basu taba ganin Biliyan 4 a zahiri ba duk yawanci a takarda ne.
Tace kuma matsalar mutane basa yawo ne shiyasa, tace amma ita tana yawo kuma ita ‘yar kasuwa ce dan haka ko a yanzu ma an bata gidajen Naira Biliyan 5 ta sayar a Abuja.