Jami’an ‘yansanda a jihar Ondo sun kama wani matashi me suna Yusuf Adinoyi bayan samunsa da kawunan mutane 8.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Abayomi Oladipo, ya tabbatar da kamen inda yace an kama wanda ake zarginne ranar Litinin bayan an kafa shingen bincike.
Mutumin na kan hanyar zuwa Akure ne kamin aka tare motarsu wadda yayi kokarin tserewa amma aka bishi aka kamoshi.
Ya amsa laifinsa inda yace a baya yana sana’ar sayar da manja ne amma rashin lafiyar mahaifiyarsa tasa ya shiga harkar sayar da kawuna.
Yace wannan ne karo na 3 da yake son sayar da kawunan inda a farko ya sayar da guda 4, sannan ya sayar da guda 3 hakanan sai yanzu zai sayar da guda 8.
Kwamishinan ‘yansandan yace za’a gurfanar dashi a kotu bayan kammala bincike.