
An ga Bidiyon yanda aka rikawa motocin ‘yan siyasa rotse a Zaria jihar Kaduna.
An ji matasa na fadin bama so, bamayi.
Saidai kowane bangare tsakanin APC da ADC na ikirarin cewa abokan hamayarsa ne akawa hakan, wasu na cewa ‘yan APC ne akawa haka yayin da wasu ke cewa ‘yan ADC ne akewa hakan.
A ranar Asabar ne dai za’a gudanar da zabe a wasu bangarori na jihar.
Akwai adawa me zafi tsakanin Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad da Gwamna me ci, Malam Uba Sani.