Friday, December 5
Shadow

Peter Obi ya buƙaci magoya bayansa da su zabi ADC a zaɓukan cike-gurbi

Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a Jam’iyyar Labour, Peter Obi ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a a Najeriya, musamman masoyansa na ƙungiyar Obidient da su zaɓi jam’iyyar ADC ne a zaɓukan cike gurbi da za a yi a gobe Asabar.

Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce, “a game da zaɓukan da za a yi a gobe Asabar, 16 ga watan 2025 domin cike gurbin wasu kujeru a jihohi 16 na Najeriya, tunda jam’iyyar LP ba ta da ƴantakara saboda kotu ta hana sanadiyyar rikice-rikicen da ke cikin jam’iyyar, ina kira ga masoyana da su su zaɓi jam’iyyar haɗaka ta ADC a jihohinsu.”

Wannan jawabin na Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta muhawara game da yunƙurin haɗakar siyasa, inda ake tunanin manyan jam’iyyun hamayya za su iya haɗuwa a guri ɗaya domin fuskantar Tinubu a zaɓe mai zuwa.

Karanta Wannan  YA SUBHANALLAH: Al'ummar Wasu Kauyuka Sama Da Ashirin Kenan A Yayin Da Suke Gudu Suna Barin Matsugùnansu Bayan Barazanar Kai Hàrì Da Riķaķken Dàn Bìndiga Kuma Babban Yaron Beĺlò Ťùŕjì, Wato Kallamu YaÝi Musu, Inda Suka Shigo Garin Gatawa Neman Mafaka

Za a zaɓen ne a jihohi 16 a Najeriya, inda za a yi zaɓen cike gurbi na sanatoci biyu, da majalisar wakilai biyar da majalisar jiha guda 9 a jihohi daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *