MAAN ta nemi taimakon EFCC, DSS da ƴansanda wajen karɓo bashin da manoman masara su ka karba.

Kungiyar Masu Noman Masara ta Najeriya (MAAN) ta ce ta na haɗa gwiwa da DSS, EFCC da ‘yansanda domin dawo da rancen shirin Anchor Borrowers da aka bai wa manoma tsakanin 2018 zuwa 2021.
Shugaban MAAN na ƙasa, Bello Abubakar, ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce yawancin manoman da suka karɓi kuɗin sun ki biyan bashin, suna ɗaukar sa a matsayin “kudin al’umma.” Ya ce ƙungiyar ta tura wasikun tuni, ta kuma kai ƙara ga wasu masu bashi, yayin da ake ci gaba da shari’o’i a kotu.
Abubakar ya bayyana cewa matsalar tsaro da ambaliyar ruwa na barazana ga noman masara a jihohi da dama, yayin da fari ya shafi wasu yankuna.
Ya roƙi gwamnatin tarayya ta samar da yanayi mai sauƙaƙa domin manoma su biya bashin, tare da rage ko yafewa ragowar kuɗin, yana kuma yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa ƙoƙarin tabbatar da samar da abinci.