
Majalisar wakilai ta bukaci dan majalisar daga jihar Jigawa me wakilar Hadejia, Auyo, da Kafin Hausa, Ibrahim Usman Auyo ya fito ya kawo shaidar cewa sai an biya kudi ake gabatar da kudirin doka a majalisar.
Dan majalisar dai yayi wannan ikirarin ne a yayin ganawa da mutanen mazabarsa.
Inda yace Ana biyan daga Naira Miliyan daya zuwa 3 kamin gabatar da kudirin doka a majalisar.
Saidai a martanin majalisar ta bakin me magana da yawunta, Akin Rotimi tace ba zata bari a bata mata suna ba, wannan ikirari na dan majalisa, Ibrahim Usman na da girma kuma zata bincikeshi ya bata hujjarsa.
Tace amma idan bai bayar da wata hujja ba, zata gabatar dashi a gaban kwamitin da’a na majalisar.