
Rahotanni daga Abuja da Legas na cewa, Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya sake rage farashin man fetur a garuruwan biyu da Naira 10.
Kafar The Cable ta ruwaito cewa ta lura a Abuja ana sayar da man fetur din akan naira N890 maimakon Naira 900, hakanan a Legas kuma ana sayar dashi akan Naira N865 maimakon Naira N875.
Kafar tace ta gudanar da wannan bincike ne a ranar Juma’a data gabata.
Hutudole ya lura Wannan ne karo na biyu da hakan ke faruwa.