
Rahotanni sun tabbatar da cewa, Jam’iyyar APC ta lashe zaben cike gurbi na Ghari/Tsanyawa, Kano.
Baturen zabe, Professor Muhammad Waziri na jami’ar Bayero dake Kano ne ya bayyana Garba Gwarmai na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 31,472.
Yayi nasara ne akan dan takarar jam’iyyar NNPP, Yusuf Maigado, wanda ya samu kuri’u 27,931.