
Jama’a Ina Neman Taimakon Kudì Domin Duk Mako Uku Sai An Yi Min Allurar Naira Dubu 250, Kuma Sai An Yi Tsawon Watanni Shida Ana Yi Min Allurar, Cewar Malam Nata’ala Na Shìirin Dadin Kowa
Fitaccen Jarumin finafinan Hausa, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a cikin shirin Daɗin Kowa yana na neman taimakon jama’a sakamkon yadda jinyar da ya ke fama da ita ta ci kàrfinsa.
Cikin wani faifen bidiyo da ya fitar, ya nemi da a taimaka masa domin a duk bayan sati uku sai an yi masa allura ta naira dubu 250,000.
Ya buƙaci jama’a da su yafe masa domin bai sani ba ko wannan jiyar da ya ke yi ba wadda zai tashi ba ne ko kuma saɓanin haka. Sannan ya ce idan akwai wanda ya masa laifi shi ya yafe masa.
Ya bayyana cewa, ciwon daji ne ya ke fama da shi na tsawon lokaci.