
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana son shiga Aljannah.
Ya bayyana cewa dalili ma kenan da yake ta kokarin ganin ya kawo karshen yakin kasashen Russia da Ukraine.
A baya Shugaba Trump ya gana da shugaban kasar Russia, Vladimir Putin sannan ya gana da shugaban kasar Ukràìnè sa shuwagabannin kasashen Turai.
A nan gaba yace zai hada Putin da Zelenskyy su yi zaman sulhu.
Tun kamin ya zama shugaban kasa yayi Alkawarin cewa idan ya ci zabe, zai tabbatar ya kawo karshen yakin.