Friday, December 26
Shadow

Sai an kawo mana dauki, Lamuran tsaro sun ta’azzara>>Inji Gwamnan riko na jihar Katsina, wanda Gwamna Radda ya barwa jihar a hannunsa

Gwamnan riko na jihar Katsina wanda gwamna Dikko Radda ya barwa jihar a hannunsa Malam Faruk Lawal-Jobe ya yi kira ga gwamnatin tarayya data kawo musu dauki a jihar game da tabarbarewar lamuran tsaro.

Wannan kira nasa na zuwane bayan harin da ‘yan Bindiga suka kai unguwar Muntau dake garin Malunfashi a jihar Katsina suka kashe mutane akalla 13 dake sallar Asuba.

Hakanan maharan sun rika harbin kan mai uwa da wabi inda kuma suka sace mutane 60, kamar yanda kafar Rariya ta tuwaito.

Hakan na zuwane a yayin da Gwamna Dikko Radda ke kasashen Turawa nema Lafiya amma an hangoshi a wasu hotuna yana daukar hoton garin da yaje.

Karanta Wannan  Na gano sabuwar hanyar samun kudin da ta fi ta Man Fetur>>Shugaba Tinubu

Gwamnan rikon, Malam Faruk Lawal-Jobe ya nemi gwamnatin tarayya data kawowa jihar dauki lura da yanda lamuran tsaro suka tabarbare tare da neman Shugaban kasa ya baiwa jami’an tsaro dokar ta baci kan matsalar tsaro a jihar ta Katsina.

Saidai Malam Faruk Lawal-Jobe ya kuma jinjinawa jami’an tsaron da yanzu haka ke aiki a jihar ta Katsina da kuma jami’an tsaron sa kai dana Bijilante, Kato da gora.

Jihar Katsina na daga cikin wanda suka fi fama da matsalar tsaro yankin Arewa inda ake kashe mutane da yin garkuwa da mutane dan neman makudan kudaden fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *